Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Shiga nan domin samun baya nai da kuma download na karatuttukan sheik ja'afar
Shiga nan domin samun bayanai da kuma dowload na karatukan sheik ja'afar
LAFAZIN MARGAYI SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM (R) GAME DA MAULUDI
.
Malam yaci gaba da cewa:
.
"Shi yasa lokacin da muke musu da wadansu yan uwa kan batun MAULIDI MAULIDI MAULIDI muka ce duk abune mai sauqi da AKHADAREE da ISHIMAWEE da IZIYYAH da RISALA da ASKAREE da MUKHUTASAR, wadannan duk littattafai ne na koyon addini da mu da ku duk muna koyon addini a cikin su amma babu daya daga cikin su da ya kawo BABI KO FASALI NA MAULIDI.
.
Yanzu muna neman illa da tasa basu kawo ba, shin sun yi mantuwa ne? Sun jahilta ne? Ko ko ba addini ba ne don haka ba su kawo ba???
.
Saboda haka cikin wadannan dole ayi daya ko dai ya kasance mantuwa sukayi? ko ko ilimin su ne bai kai ba? Koko a fahimtar su shi din ba addini ba ne? Shiyasa basu kawo shi ba?"
.
Mallam har ya rasu baku kawo masa wadannan amsoshin ba, to mu har yanzu muna jira ku kawo mana, idan har kun gagara kawowa to muna kiran ku da kuji tsoron Allah ku dawo kubi karantarwar Alqur'ani da Sunnar Annabi (saw) sai ku samu hutu a rayuwar ku ta duniya da lahira.
.
YA ALLAH KA JIQAN SHEIKH JAFAR KA KAR6I SHAHADAR SHI.
.
LAWAL MAMMAN BILBIS CHAIRMAN JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO MUNICIPAL,

10307367 512176872258921 4580044614639290014 n


@@ MENE SAHIHIYAR MAGANAR MARIGAYI SHEIK JA'AFAR (R) CEWA DUK CIKIN AL-KUR'ANI BA INDA AKACE ASO ANNABI (s.a.w) kashi na 1.
.
Ina mai farawa da sunna Allah maikowa mai komai makadaici kuma mamallakin dukkan komai bayan haka
.
Nayi nufin yin wannan dan rubutu ne domin ganin irin yada ma'abota 6ata yan bidi'a da mushrikai suketa yawo da sautin muryar marigayi sheik ja'afar mahmud Adam Kano (Rahimahullah) waddad suka yanketa daga wani karatunsa inda suke cewa yace' Duk cikin kur'ani babu ayar da tace aso Annabi wanda wannan rashin adalci ne sbd ba'abari anji cijakken bayanin da ya kawo ba kawai se aka yanke iya gun domin aci mutuncinsa kuma koda asatinnan naga wani mushriki ya kawo maganar ashafin facebook don haka naga dacewa rubuta cikakken bayanin kamar yadda sheik ja'afar yayi da bakin sa xan kawo amman ayoyi kawai xankawo fassararsu ne kamar yadda ya fassara baxan jawo bakin ba Allah yabamu ikon Amfana ga Abinda malam yake cewa
.
''CIKIN AYOYIN AL-KUR'ANI A IYAKACIN KARAMIN ILIMIN DA NAKE DASHI. BANGA AYAR DA TAZO TACE KUSO ANNABI (s.a.w) BA!!''
.
Wannan maganace mai nauyi amma kuma magana ce ta ilmi. Amman shin wannan yana nufin kar asoshi?? Ba mai hankali da zai fahimci haka! Sai in mutum yana da mummunan nufi. Yaso ya birkita zancenka ba dai-dai ba to sai ya fahimci haka wannan ba yadda ka iya dashi Amma gaskiyar magana dai ba aya da tazo tace:-
,
''Ya ku jama'a kuso shi.''
.
Saboda Ubangija da ya halicce mu yasan yayi masa tattalin da ko ba'ace a soshi ba za'a soshi idan kai mu'umini ka soshi a matsayinka na mu'umini. Kafiran da suka soshi fa? Kaga ba wai sun dogara bane kan wata aya da tace asoshi . To amma ayoayi sun zo sau yafi a irga wadanda sukace ayi masa da'a sabida me''
.
Zamu cigaba akashi na 2
.
.
Allahu Akbar Allah yajikan malam da rahamar sa
.
Www.sunnahsak.mywaog.com
.
Yan uwa a taimaka da share don sauran yan uwa


@@ MENE SAHIHIYAR MAGANAR MARIGAYI SHEIK JA'AFAR (R) CEWA DUK CIKIN AL-KUR'ANI BA INDA AKACE ASO ANNABI (s.a.w) kashi na 2
.
Cigaba
.
Marigayi Sheik ja'afar (Rahimahullah) ya cigaba da cewa:-
.
''Saboda ubangiji ya haliccemu ya san yayi masa tattalin da ko ba ace asoshi ba xa'a soshi . Idan kai mumini kasoshi a matsayinka na mumini kafiran da suka soshi fa? Kaga ba wai sun dogara ba ne kan wata aya da tace asoshi. To amma ayoyi sun zo sau yafi a kirga wadanda sukace ayi masa da'a sbd me?
.
Sbd Abinda ke gasgata so din shine da'a ko kace ina son shi in baka yi masa da'a ba babu son . Son bai zama gaskeba! Kuma yanzu ko mace ce kace kana sonta . Kaje kabiya sakai ka auro ta ka ajiye ta agida amma baci ba sha ba kiwon lafiya in bata da lafiya baruwanka da kowa. Ana haka sai ta kai kara aka ce ka sake ta ko kaciyar da ita sai kace:-
.
''Wallaho Al-kali ba zan iya rabuwa da ita ba saboda ina bala'in sonta''
.
Karya kake! Kana son ta ka barta taba kwana da yunwa kabarta bata daafiya baka ji kanta ba???
.
''Sbd dalilan da suke nuna so din ba'a gani ba atare da kai don haka loakacin da mutum yace:-
.
''INA SON MAN ZON ALLAH (s.a.w)!'' Sai akalli alamar so din atare da shi wato yana yi masa da'a ko kuwa?? Shi yasa Allaah yake maganar...
.
Zamu cigaba InshaAllahu a kashi na 3
.
Ya Allah ka lullu6e kabarin sheik ja'afar da rahama
.
Www.sunnahsak.mywapblog.com
.
Y'an uwa ataya da share face book twitter WastAp da sauaransu


@@ MENE SAHIHIYAR MAGANAR MARIGAYI SHEIK JA'AFAR (R) CEWA DUK CIKIN AL-KUR'ANI BA INDA AKACE ASO ANNABI (s.a.w) kashi na 3
.
Cigaba
.
Malam ya cigaba da cewa:-
.
''Lokacin da mutum yace ''INASON MANZON ALLAH (s.a.w) sai akalli alamar so din a tare dashi wati yana yi masa da'a ko kuwa? Shi yasa sai Allah yake maganar da'a:
.
''Kace kuyi da'a ga Allah da manzon Amma idan sun juya baya to lalle ne Allah baya son Kafirai''
,
(suratu Al-imran aya ta 32)
.
''Yaku wadanda suka yi imani! Kuyi da'a ga Allah kuma kuyi da'a ga manzo da ma'abota al-amari a cikinku''
.
(suratun nisa'i aya ta 59)
.
''Kuma wadanda sukayi da'a ga Allah da manzo to wadannan suna tare da wadanda Allah yayi ni'ima Akansu daga Annabawa da masu yawan gasgatawa da masu shahada da salihai kuma wadannan sun kyautatu da zama abokai''
.
(suratun nisa'i aya ta 69)
.
''Wanda yayi da'a ga manzo to yayi da'a ga Allah''
.
(suratun nisa'i aya ta 80)
.
''Kuma kuyi da'a ga Allah da manzon sa kuma kada kuyi jayayya har ku raunana kuma karfinku ya tafi kuma kuyi hakuri lallai Allah yana tare da masu hakuri''
.
(suratu Anfal aya ta 46)
.
''Ku amsa kiran da manzon Allah (s.a.w) yake muku'' wato shela da kururuwa da yayi cewa:-
.
(suratu anfal 24)
.
''Na horeku da bin sunna ta da sunnar halipopi shiryayyu''
.
''Ku amsa! Idan ya kiraye ku izuwa ga Abida rayuwar kune''
.
(suratu Anfal aya ta 24)
.
''Kuma Allah da manzon sa ne mafi can - cantar su yarda dashi idan sun kasance mu'uminai''
.
(suratu tauba aya ta 62)
.
Zamu cigaba inshaAllahu
.
Ya Allah muna rokonka ka gafaratawa shiek ja'afar Allah ka sanya shi A Al-jannarka Allah ka lullu6e kabarin sa da rahamarka
.
Www.sunnahsak.mywapblog.com
.
Yan uwa a taimaka da share


@@ MENE SAHIHIYAR MAGANAR MARIGAYI SHEIK JA'AFAR (R) CEWA DUK CIKIN AL-KUR'ANI BA INDA AKACE ASO ANNABI (s.a.w) kashi na 4
.
Cigaba
.
Malam ya cigaba da cewa Allah (s.a.w) yace;-
.
''Kace ''Kuyi da'a ga Allah kuma kuyi da'a ga manzo idan kun juya . To akansa abin da aka aza masa kawai . Kuma akanku akwai abinda aka aza kawai kuma idan kun yi masa da'a zaku shiryu kuma babu abin da ke akan manzo , face iyar da sako bayyananne''
.
(suratun nur aya ta 54)
.
''Yaku wadanda sukayi imani kada ku gabatar da komai gaba da Allah da manzonsa''
.
(suratu hujrat ayata 1)
.
''Kada ku daga sautukanku sama da sautin Annabi''
.
(suratu hujrat aya ta 2)
.
''Kada ku sanya kiran manzon Allah tsakaninku kamar kiran sashenku ga sashe''
.
(suratu nur aya ta 63)
.
Ma'ana dai a nan za'aga cewa ayoyin sunada yawa :ku bishi : ku makalkale ma sunnarsa; kuyi masa da'a cikin abin da yayi muku dadi ko inda bai muku dadi ba cikin abinda kuke so ko wanda ba kwaso cikin abinda ya sa6awa shugabannin ki ko yayi dai-dai da Abinda suke so kubishi kuyi masa da'a SALLALLAHU ALAIHI WA AALIHI WASSALAM!
.
Kaga kenan da'a (biyayya) itace babbar Alama ta ina son Annabi (s.a.w) Wallahi Tallahi! Duk wanda yace yana son manzon Allah (s.a.w) Kuma baya yi masa da'a da'awarsa Karya yakeyi! Koda yayi baiti dubu sau dubu na yabo da madahu ga Annabi (s.a.w) Karya yake yi
.
Karin bayani dan gane da waka shine...............''
.
Ku biyo mu a kashi na gaba don jin cigaba
.
Visit www.sunnahsak.mywapblog.com
.
Ya Allah ka gafartawa sheik ja'afar da rahama


@@ MENE SAHIHIYAR MAGANAR MARIGAYI SHEIK JA'AFAR (R) CEWA DUK CIKIN AL-KUR'ANI BA INDA AKACE ASO ANNABI (s.a.w) kashi na 5
.
Cigaba.
.
Sheik ja'afar (rahimahullah) ya cigaba da cewa:-
.
''Karin bayani dan gane da baitin waka shine sahabbai suna da yawa kaddara ba wani sahabi a duniya se wanda suka je yakin badr . Misali dari uku da gima sa.....
.
Kaddara babu wani sahabi sai wadanda sukayi Bai'atu-ridhwan, su dubu daya da dari hudu 1400, Ace wannan shine adadi mafi yawa na sahabbai adadin da daga shi sai ayi yo kasa to acikin sahabban nan dubu da dari hudu da-wa- da-wa ne , suke da kasida ta Annabi (s.a.w)??
.
To ballantana ba wadannan ne kadai sahabbai ba domin sahabbai zasu kai dubu dari biyo 200,000 Akwai wanda tsakanin sa da Annabi (s.a.w) kawai a Hajjatul-Wadaa'i ne , kafin nan bai ta6a ganin shi ba kuma daga rannan bai sake ganin shi ba har ya bar duniya. Wannan mutum kuwa sunan shi sahabi! Tunda yaga Annabi , yayi imani dashi kuma ya mutu Kan imanin, bai yi ridda ba sai da wadanda suke kusa da Annabi (s.a.w) sun fi shi falala, tunda su sun kasance tare da Annabi (s.a.w) ko waneokaci. Allah yana cewa;
.
Wanda ya ciyar a gabanin cin nasara kuma yayi yaki daga cikin ku baya zama dai-dai (dawanda bai yi haka ba),
,
(suratu Hadeed aya ta 10)
.
Don haka ba dai-dai suke ba wajen falala da matsayi
.
Kuma Allah yana cewa;
.
''Masu zama don barin yaji daga mu'uminai banda ma'abota larura da masu jihadi a cikin hanyar Allah da dukiyoyinsu da rayukansu. Basu zama dai-dai. Allah ya fifita masu jihadi da dukiyoyinsu Allah yayi musu zama ga daraja . Kuma dukkansu. Allah yayi musu al-kawari da abu mai kyau. Kuma Allah ya fifita masu jihadi akan masu zama da lada mai girma''
.
Ba dai-dai suke ba! Amma tare da haka wancan mutumin da yaga Annabi (s.a.w) sau daya sunan sa sahabi to yanzi ace cikin mutanen da sun kai dubu dari biyu amma wadanda suka shahara da baitin waka da sukayi ta yabon Annabi (s.a.w): Hassanu bin Thabit, Abdullahi bin Rawahaa Sai Alkhansa'u. To daga nana fa sai wa?? Sauran da basi ta6a yin baitin waka ba basa son Annabi (s.a.w) kenan?? Kuma yanzu idan ka......''
.
Zamu cigaba Insha Allahu
.
Ya Allah ka gafar tawa malam da rahamar ka


@@ MENE SAHIHIYAR MAGANAR MARIGAYI SHEIK JA'AFAR (R) CEWA DUK CIKIN AL-KUR'ANI BA INDA AKACE ASO ANNABI (s.a.w) kashi na 6 kuma na karshe
.
Cigaba.
,
Sheik Ja'far (rahimahullah) ya cigaba da cewa
.
''Yanzu a cikin mutanen da sunkai dubu dari biyu amma wadanda suka shahara da baitin waka da sukayi ta yabin Annabi (s.a.w); Hassanu bin Thabit . Abdullahi bin Rawahaa sa Al-khansa'u . To daga nan fa sai wa?? Sauran da basu ta6ayin waka ba basa son Annabi (s.a.w) kenan?
.
Kuma yanzi Idan ka duba wadannan sahabbai guda uku 3 da aka lissafa wadanda suka shahara da waka . Ko wani kari da za'a iya kawowa. Za'aga basa cikin guda hudun 4 da man zon Allah (s.a.w) yace:
.
''ALAIKUM BI SUNNATIY WA SUNNATI KHULA FA URRASHIDEEN''
.
Basa cikin goman da akayi musu Al-bishir da Al-janna. Ko shakka babu suna cikin sahabbai kuma suna da falala.
.
Hikimar dake cikin nan ko darasin da mai hankali ya kamata ya dauka, shine: Ashe ba baitin waka ne abin da ake samin fala da shi ba , ko ake yin fice dashi wajen kaunar Annabi (s.a.w). A'a Da'a biyayya shine babban Abinda ake yin fice da shi wajen lallai wane masoyin Annabi ne abinda duk yake yi yana kwatanta rayuwar sa ne data Annabi yana kokarin koyi da Annabi wannan shine hakikanin soyayya . Amma kayi baitin waka guda dubu 100, kuma ka sa6a hadisan manzon Allah dubu to meye amfanin ka meye amfanin baitin wakar ka, kuma cikin baitin wakar ma baka dora su kan sikelin Allah yace, Annabi yace ba, Wadansu akwai shirka wadansu akwai guluwwi wadansu akwai abubuwa da suke munana ladabi tsakaninka da ManzOn Allah (s.a.w). Jahiltar sunna ya gadar maka ha!
.
Saboda haka ya kamat ayi hattara da'a itace alama farko cikin alamimin son Manzon Allah (s.a.w).''
.
Ya #Allah ka gafartawa sheik ja'afar ka lullu6e kabarin sa da rahamarka

***LAFAZIN SHEIK JA'AFAR {rahimahullah}***
.
Source:- www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com/sheik%20ja_afar%20mahmud%20adam%20_rahimahullah_
.
WATA RANA ASH-SHAIKHUL MUFASSIR, AL-MUJTAHID, ABU- SALIM, JA'AFAR MAHMUD ADAM KANO (RAHIMAHULLAH) yake fada a cikin karatunsa
.
.
''KUMA BAN YARDABA GA DUKKAN WANI WANDA ZAIJI WANI YA ZARGENI,KO YA ZAGENI,KO YA MIN RADDI. YACE ZAIYI ADAWA DASHI KO YAYI FADA DASHI KO YAYI RIGIMA DASHI.
.
DOMIN DUKKAN WANDA YAYI RADDI,DAYA DAGA CIKIN BIYU NE.
KOYA ZAMTO YA FADI GASKIYA CIKIN RADDINSA,, SAIMU KARBETA TUNDA GASKIYA YA FADA.
.
KOYA ZAMTO KARYA YA FADA CIKIN RADDINSA, TO WANNAN KUMA DONME ZAKA SHAGALA DASHI.
.
KUMA DUKKAN WANDA YA FADA MAKA BAKAR MAGANA KAI AKARAN KANKA KOYA ZAGEKA.
.
DAYA DAGA CIKIN BIYUNE.
.
KODAI YA ZAMTO KA CHANCHANCI ZAGI SHIYASA YA ZAGEKA,
TUNDA KA CHANCHANCI ZAGI,YANZU ZAGIN DAYI MAKA SAIYA SA KA GYARA KUSKURENKA.
KOYA ZAMTO BAKA CHANCHANCI ZAGIBA YA ZAGEKA,TO KAGA WANNAN YA RAGE MAKA LAIFUKANKA KENAN.
.
DON HAKA DONME ZAKA DAMU.
.
.
.
#Allahu Akbar kunji mazaje gwanina ba'abinka bashin hujja
.
Yaaaaaa Allah ka gafartawa sheik ja'afar mahmud Adam kano
.
Allah ka lullu6e kabarinsa da rahama


Sheik jaafar 11

Shawarwari 52 daga bakin Marigayi Sheikh
Jafar Mahmoud Adam Kano zuwa ga ma'aurata.
.
Da sunan ALLAH mai gamammiyar rahama mai jinkai, tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahama, da alayansa, da sahabbansa, da duk wadanda suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar tashin al-kiyama.
.
Bayan haka,
.
shakka babu, a wannan zamani 'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda aurensu yake yawan mutuwa, bayan kuma, an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani.
.
Ga wasu Shawarwari wadan da idan mata sukayi la'akari da su insha ALLAH za'a samu kyautatuwar zaman aure. Muna addu'ar ALLAH ya bada ikon kiyayewa.
.
1- Aurenki ya zama domin neman yardar
ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.
2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben
mijin Aure.
3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren
wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa
harma da dangantakarsa.
4- Ki zama mai riko da addini a gidan
mijinki.
5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar
mijinki. Hakan na da matukar hadari a
rayuwa aure.
6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.
7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.
8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya
kala-kala.
9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-
kala.
10- Ki zama kin iya barkwancin magana
wajen baiwa mijinki dariya.
11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk
abinda mijinki ya baki.
12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma
da kuma lokacin kwanciya barci.
13- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki,
abincinki, da sauransu.
14- Ki dinga girmama Iyayan mijinki da 'yan
uwansa da abokansa.
15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.
16- Kada ki zama mai satar fita unguwa.
17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana
daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin
Hausawa.
18- Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya
baki.
19- ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.
20- ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da
safe, rana, dakuma dare.
21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.
22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki
akan duk wani al'amari da zaki yi.
23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar
mijinki.
24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki,
kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a
duk lokacin kwanciya.
25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki
kafin dawowar mijinki.
26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki
gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da
kiyayya.
27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin
kafarki da kuma zanen kitso.
28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda
ba shida ikon saye.
29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke
dukkan wani hukunci.
30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake
yi miki fada ko Nasiha.
31- Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.
32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki,
naki ko na mijinki suna wari.
33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na
zuwa unguwa.
34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa
mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.
35- Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin
sirrin dake tsakaninki da mijinki.
36- Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa
da tattaunsan harshe, da murya mai karya
zukata.
38- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun
sha'awa ko soyayya.
39- Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi
hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.
40- Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda
kika mallaka a gidan mijinki.
41- Kada ki zama mai kwauron baiwa dangin
mijinki abinda ya umarceki da a basu.
42- Kada ki zama mai yin dare wajan girki.
43- Kada ki zama uwar adashi ba tare da
sanin mijinki ba.
44- kada ki zama mai yawan fada da
makwabtanki.
45- Kada ki kasance mai yawan zagi ko
Ashariya.
46- Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin
laifin da mijinki yake miki.
47- Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar
Iyayan mijinki da 'yan uwansa.
48- Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna
masa bacin ranki a gaban iyayanki ko 'yan
uwansa.
49- Kada ki ringa daga murya sama idan
kuna sa-in-sa da mijinki.
50- Kada ki ringa baiwa 'yan uwan mijinki
labarin laifukansa.
51- kada ki ci wani abu da mijinki baya son
warinsa misali tafarnufwa.
52- Ki dinga yiwa mahafiyar mijinki Ihsani da


***LAFAZIN SHEIK JA'AFAR***
.
.
.
IDAN BAKA SHIRYA KA MUTU BA...
.
.
Marigayi Malam Ja'afar a wata Lakcar sa ya na cewa:O
,
"Idan kai kana ganin cewa ba ka shirya ka MUTU ba, kana da inda zakai don kar ka mutu, to don Allah idan ina karatu ko ina huduba kadaina zuwa sahun gaba, don idan an harbeni kar jini ya vata ma shaddarka da kake ado da ita.
Don Allah idan ina karatu kadaina zuwa sahun gaba, idan ina huduba kadaina zuwa sahun gaba, dan idan an harbeni kar jini ya fallatsarmaka ya vata ma shaddarka da kake ado da ita"
.
.
.
Allahu akbar! Haka kuwan akai, cikin ikon Allah asubahin wata juma'a a masallacin sa dake dorayi, wasu Y'an ta'adda la'anannu y'an jahannama suka harbe Malam har lahira. Inda muryarsa ta dinga daukaka tana cewa
.
.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN LA ILA HA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH"
.
.
Duk jama'a Makota masallaci da wadanda suke nesa da Masallaci suna jinta cikin amsa kuwar Masallacin.
.
.
Allah sarki Malam Katafi amma har a yanzu kana raye,
.
.
Allah ya jikan Malam ya gafarta Musu shi da dan uwansa Malam Albani Zariya.
Da ma sauran Al'ummar Musulmi baki daya


***LAFAZIN SHEIK JA'AFAR***
.
.
.
''Duk wanda yazo yace mana wai mu kyale musulmi mu za6i christa tofa son zuciya ya fada mana
.
Na fadi wannan magana a kano zan sake mai-maita ta yanzu
.
Ka san a kano ni akwai wasu y'an darika tun bara waccan sunce sun yankemin hukuncin kisa
.
Tun tuni sukace sun yanke min hukuncin kisa waye da waye har program akai a radio live akai zage-zage da haya niya da cin mutunci da sauran su
.
Duka wannan malaman sun kasa suka nemo mawaka nace:- Aiki kenan
.
Ma'ana malaman sun kasa se aka komo kan mawaka.
.
Amman wallahi tallahi duk wannan Abin be sa na canza Abinda nake ganin shina fahimta Kur'ani da hadisi ba .
.
Abinda nace dasu :- Tabbas idan aka zo za6e A wuri ga musulmi tanta garya wanda yake ana sa ran kwatanta gaskiyarsa ga wani ri6a6a-ri6a6a to zan za6i wannan tantagaryar na kyale ri6a6a-ri6a6ar
.
Idan aka zo za6e ga Christa ga MUSULMI dan tijjaniyya ga MUSULMI dan kadiriyya
.
Wallahi tallahi musulminnan dan tijjaniyya ko dan kadiriyya zan za6a ba zan za6i christa ba
.
Idan wani malami yace shi baze za6eni ba ni dan Izala ne Ahlussunnah ne yanada hujja da ze fada a gaban Allah
.
Amman ni in nace a za6i christa a kyale dan darika bani da hujjar da zan fada a gaban Allah''
.
.
.
Allahu Akbar ‪#‎ Allah_Akbar‬Allahu Akbar
.
Kunje malamaiba yan tamore ba ba yan son zuciya ba
.
Ya ‪#‎ Allah‬ka kar6i shahadar sheik ja'afar Allah kai masa rahama

***TARIHIN SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM A LOKACIN RAYUWARSA***
.
.
Yau lekawa nai taskata se nai kaci6is da tarihin gwani tun a lokacin rayuwarsa muna Addu'ar Allah ya kar6i shahadar malam ya gafartamasa kura-kurensa
.
.
An haife shi ranar 12 ga watan Fabrairu shekarar1960, a garin Daura cikin jahar Katsina a Nijeriya.
Yayi karatun Al-qur'ani a gidansu a wurin mijin yayarsa wato Malam Haruna. Daga nan sai aka kawo shi unguwar Fagge a Kano wurin Malam Abdullahi, ya fara haddar Alkur'ani a gida sannan ya kammala ananKanoa 1978. Daga nan sai Malam ya shiga makarantar Arabic school karkashin cibiyarEgyptianCulturalCenterdakeBello Dandago Roada 1981. A wannan lokaci, Malam yana zuwa makarantarAdultSchooldake Shahuci, da daddare, ita kuma Egyptian Centre da yamma.
Ya kammala a shekarar 1984, wannan ya bashi damar shigaGovernmentArabicTeachers CollegeGwale a 1984, ya kammala a 1988. Daga nan ne kuma Malam ya samu shiga Jami'ar Musulunci ta Madina a 1989 zuwa 1993. Daga cikin Malamansa akwai Sheikh Abdul Rafi'i, Dr. Mahmud Abdul Haliq sai Dr. Khald As-Sabat.
Bayan Malam ya dawo daga Madina ya cigaba da karatu a Jami'ar Bayero daga baya wasu matsaloli suka hana shi cigaba. Amma a halin yanzu yana yin digirinsa na biyu a 'InternationalUniversityofAfrica', dakeSudan.
Bayan Malam ya dawo daga Madina ne ya kafa Makarantar Usman Bin Affan daga nan ta samu cigaba ta zama cibiya mai zaman kanta a 1995. Sai darussa da Malam yake gabatarwa anan Usman bin Affan, na farko akwai karatun tafsiri ya da yake gabatarwa a ranar jumma'a tsakanin magariba da isha'i, ranar asabar karatun nahawu da balaga da safe da misalin8:00amzuwa 9:30am. Sannan kuma karatun sirah ranar lahadi a Masallacin Almuntada dake Dorayi tsakanin magriba zuwa isha'I, sai laraba kuma da yake gabatar da tafsiri a Masallacin Beirut, tsakanin magriba zuwa isha'i da kuma darussan da Malam yake gabatarwa a makaranta.
Bayan haka, Malam yana gabatar da tafsiri aMaiduguria watan Azumi kuma shekaratarakenan da farawa.
A halin yanzu Malam shine shugaban cibiyar Usman Bin Affan Islamic trust kuma limamin jumma'a na Masallacin Almuntada dake dorayi aKano.
Malam yana cikin mambobin kwamitin Malamai wato "Ulama Consultative"ZamfaraStatedaBauchiState. Haka kuma, Malam yana gabatar da shirye shirye a gidajen radio da talabijin da yawa, amma kadan daga cikinsu akwai na Radio Kaduna, Bauchi Radio corporation, CTV Kano, dana DITV Kaduna NTA Borno, OITV Damaturu, NTA Yola, da sauransu.
Malam yana da iyali ( mata biyu) da 'yaya (biyar) kuma yana zaune ne a unguwar Gadon kaya cikin birninKano.


Via...Ismail Ishaq Zamfara yace;
.
Wata rana Sheikh Jaafar Mahmoud Adam
RAHIMAHULLAH yana karatun Tafseer a Masallacin Beirut Road a Kano sai wani baturen kasar Ingila ya zo zai Musulunta.
.
Baturen yace ya zo ne daga Yankari wajen shakatawa da ke Bauchi, baturen yayi bayanin cewar shi ba wa'azi akai masa da
ya musulunta ba, yace a dalilin karance - karance da bincikensa ya fahimci Addinin Musulunci gaskiya ne.
.
Baturen ance har
Aure yayi a Bauchi daga bisani ya koma Ingila shi da matarsa a can yacigaba da binciken addinin Musulunci.
.
.
.
Kwatsam rannan muna kallon Tashar Huda sai ga wannan Baturen yana wa'azi yana karanto
ayoyin al-qurani yana fassarawa.
.
Wanda muke zaune muke kallo tare da shi Alhaji Mustapha Dan Chanji shi ne ya gane baturen lokacin da ya ganshi kuma yaga
sunansa yaga sunan da Malam Jaafar ya rada masa na Abubakar shi ya cigaba da amsawa.
.
Alhaji mustapha yace min kaga su turawa idan sun musulunta da gaske suke yin Musulunci.
.
Allah ya tabbatar da mu akan shiriya ta gaskiya.
.
Allah kuma ya jikan Malam Jaafar Mahmoud Adam.

koma saman shafi

→Labarai
1234...9899100»

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 615865

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358

    The Soda Pop